Ban bi Baba na Atiku mun koma PDP ba, inji ’yar sa Fatima

1

Babbar ’yar Atiku Abubakar, Fatima, ta bayyana cewa ba ta bi mahaifin ta ta canja sheka daga jam’iyyar APC ta koma PDP ba.

Fatima Atiku-Abubakar, wadda ita ce Kwamishinar Lafiya ta jihar Adamawa, ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a halin yanzu al’amurran ayyukan da ta sa a gaba su ne a gaban ta ba maganar canza sheka da mahaifin ta yayi ba.

Ta yi wannan jawabi ne kwana daya bayan jaridar THE SUN ta ruwaito cewa Fatima ta ajiye mukamin ta na kwamishina a jihar Adamawa, ta bi mahaifin ta Atiku cikin PDP.

Fatima mai shekaru 45, ita ce babbar ’yar Atiku, an nada ta kwamishinanar harkokin lafiya ta jihar Adamawa a cikin Agusta, 2015.

Idan za a iya tunawa, a lokacin da aka nada ta kwamishina, ta bayyana cewa ba ta bukatar albashi ko alawus ko na sisi, ta je ne don ta yi wa jihar ta ta haihuwa ayyuka domin kishin jihar da kuma kishin kasa.

An buga labari a jaridar THE SUN ta jiya Talata cewa Fatima tare da wasu kwamishinoni 8 sun sauka daga gwamnatin Jibrila Bindow, sun bi Atiku zuwa PDP.

Baya ga Fatima da ta karyata labarin a sakon text da ta yi wa PREMIUM TIMES, wasu kwamishinoni biyu ma da aka tambaya sun tabbatar da cewa ba su fice daga cikin gwamnatin APC ba.

Share.

game da Author