Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan da za a sake yin zabe kuma tabbas zai lashe wannan zabe domin irin jama’ar da ya gani a Kano yau suna yi masa Maraba.
Buhari ya fadi haka ne a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, jim kadan bayan ya sauka a birnin Kano.
Bayan haka kuma Buhari ya yi wa fursinoni 500 afuwa.