An gurfanar da wani magidanci dan shekara 65 da aka kama da laifin yin lalata da wani yaro dan shekara 15 a jihar Neja.
An kama magidancin a daidai ya na aikata wannan alfasha da yaron ne a gidan sa.
Bayanai sun nuna cewa ya rude yaron ne tun daga kauyen Karimo dake babban birnin Tarayya, Abuja zuwa garin Minna da alkawarin zai nema masa aikin to.
Da ya kawo shi garin Minna sai ya ajiye shi a dakin sa ya na ta aikata hakan da yaron.
Daketan hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja Abigail Unaeze ta ce mutumin ya amsa laifin sa.