Jam’iyyar APC a rude take, ta Kan manta itace ke Mulki ba adawa ba – Tanimu Turaki

0

Mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara, Tanimu Turaki a tattaunawa da ya yi da Sani Tukur na PREMIUM TIMES, ya fadi wasu dalilai da yake ganin sune ummul- aba-i-san tabarbarewar tattalin arzikin Kasar nan da rashin iya kamun ludayin jam’iyyar APC da ke mulki yanzu.

Tanimu ya ce gwamnatin APC ta ruguza ginin da PDP ta yi a shekarun da tayi ta na mulki.

Ya karyata korafin da APC ke yi na wai ko da suka hau mulki tattalin arzikin Kasar nan a lalace suka sameta.

“To ai dalili kenan na ce ita APC har yau ta na yi wa kanta kallon jam’iyyar adawa. Lokacin da PDP ta kama mulki, mun gaji tattalin arziki wanda kusan a mace ya ke murus, sakamakon dadewar da kasar nan ta yi a karkashin mulkin sojoji. Jama’a da dama ba su da amanna kan tattalin arzikin mu. Masu zuba jari daga kasashen waje duk sun nade kayan su sun gudu inda su ka fito.

“Likitocin kasar nan, lauyoyi, masana kimiyya da masu magunguna duk suka rika gudu neman aiki a wasu kasashen ketare. Duk inda suka je, sai a ga su ne a sahun gaba wajen kwarewa a duniya, kuma suka rika samun kudi sosai.

“To idan mutanen kasar ka na guduwa neman aiki a wasu kasashe, kenan ba su da yakini kan kasar su kenan. Ta yaya za ka yi tunanin ‘yan wata kasa za su shigo kasar ka su zuba jari?

“A cikin wannan mawuyacin halin fa PDP ta karbi mulki. Me muka fara yi? Sai muka fara nuna wa ‘yan Najeriya lallai mu yarda da kanmu tukunna cewa mu ma a kasar nan za mu iya cimma komai.

Tanimu ya ce a haka ne PDP ta mai da hankali wajen farfado da kishin kasa a zukatan mutane, ta fara tsare-tsaren samar da jari da abubuwan dogaro ga al’umma. Daga karshe sai ga shi an samu yalwa a Najeriya. Aka maida noma ya zama hanyar neman kudi da kasuwanci, maimakon hanyar cin abinci kadai.

“Su kuma ‘yan Najeriya da ke kasashen waje sai suka rika tururuwar dawowa gida su na zuba Karin su na bilyoyin nairori.

“Da wannan sai baki daga kasashen waje suka rika biyo su Nijeriya su ma su na zuba jarin su. A matsayin mu na gwamnati, sai mu ka samar musu wata sa’idar samun damar cimma nasara a saukake. Su ka samu tabbacin cewa idan suka yi shuka, to alheri mai yalwa za su girba ba dusa ba.

“Ta dalilin haka muka yi nasarar inganta tattalin arzikin Najeriya ya zama mafi karfi a Afrika.

“Idan kuma su na ganin ba gaskiya na ke fada ba, ai yanzu su ne a kan gwamnati, za su iya bincikawa su tabbatar da haka.

“A tuna, daga nan sai manyan kamfanoni irin su MTN suka shigo Najeriya da sauran kamfanonin hada-hadar man fetur da gas da sadarwa, kiwon lafiya da harkojin noma.

“Amma tun APC ba ta cika watanni uku a kan mulki ba sai masu jari a kasar nan suka fara tserewa. Mutum ya shigo kasar mu ya zuba jari, amma daukar riba sai ta gagara. Aka wayi gari kamfanonin gine-gine suka rika korar ‘yan Najeriya su na rufe kamfanonin.

“Daga nan fa tattalin arziki ya lalace, kuma sun san haka, ba kuma za su iya murje idanu su ce ba haka ba ne.

“To yanzu a wane hali a ke ciki? An wayi gari mu da a lokacin PDP Najeriya ce lamba 1 wajen karfin tattalin arziki a Afrika, an wayi gari yanzu mu na wajen na 30. Kowa sai ficewa ya ke yi a kasar nan.

“Ka dubi yadda a yanzu harkokin Ma’aikatar Man Fetur ta lalace da harigido da bulkara, har shi kan sa Ibe Kachukwu ya yi maganar wasu kamfanoni uku. Idan har irin wannan harkallar na faruwa a wuri daya, sai ka yi tunanin abubuwan da ke gudana a sauran bangarorin.

“Kada ma a tsaya yin maganar zargin wuru-wurun da ke faruwa yanzu a Babban Bankin Nijeriya, CBN ta hanyar canjin kudi. Sarkin Kano ya yi wannan maganar, kuma har yau ba a yi komai a kan matsalar ba.

“Akwai wasu daidaikun mutane a kasar nan, wadanda a yau su ke kwanciyar su a gida, amma a su ke samun bilyoyin nairori ta dalilin canjin kudi da Babban Bankin Nijeriya, CBN ke ba su.

“A halin yanzu dai tubali da dirkokin Gina ginshikin tattalin arzikin kasar nan duk sun karye. Ina tausaya wa PDP idan ta dawo kan mulki, domin ban san irin munin da za ta tarar APC ta yi wa tattalin arzikin kasar nan ba. APC ta maida mu shekara 20 baya.

“Dole sai mun sake gina amanna da kasar mu ga baki masu zuba jari, domin su sake amincewa da mu su dawo, har ma wasu su shigo.

“Amma idan aka dubi halin da kasar nan ke ciki, APC bai kamata ta rika borin-kunya ba, domin ta san ta rigaya ta karya tattalin arzikin da PDP ta gina a cikin shekaru 16.

Share.

game da Author