Wani babban Jami’i a gidauniyar ‘Project Blue PWc’ Andrew Nevin ya ce kashi 70 bisa 100 na magungunan dake yawo a Najeriya jabu ne.
Ya fadi haka ne a taron da kungiyar masu sarrafa magunguna a Najeriya PSN ta shirya a Umuahia jihar Abia.
Ya bayyana cewa a nahiyar Afrika mutane 100,000 ne suke rasa rayukan su duk shekara dalilin amfani da jabun magani.
Saboda haka ne ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar NAFDAC da su daura damara wajen kawar da jabun magunguna a kasar nan.
Nevin ya kuma jinjinawa gwamanti kan kokarin da ta ke yi wajen rage yaduwar cututtukan da ake kama su ta hanyar jima’I da kuma mutuwan yara kanana.
Bayan haka gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya yi kira ga hukumar NAFDAC da su sa ido kan yadda ake sarrafa magungunan gargajiya a kasar nan musamman wadanda ba a tabbatar da ingancin su ba.
Ikpeazu ya kuma yi kira ga gwamanti da ta nemi hanyoyin rage shigowa da magunguna daga kasashen waje domin farfado da masana’antun sarrafa magunguna a kasar nan.
Ya kuma yi kira ga masana’antun sarrafa magunguna na kasa da su rage farashin magunguna domin talakawa.
Discussion about this post