Tsohon kakakin fadar gwamnatin tarayya, Segun Adeniyi, ya bada hakuri dangane da tankiyar da aka yi tsakanin sa jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasa, inda suka hana shi shiga domin ya halarci taron kaddamar da littafi.
Adeniyi, wanda shi ne kakakin yada labarai na tsohon shugaban kasa marigayi Umaru ’Yar’Adua, ya bada hakurin ne a shafin sa na Twitter, bayan da ya shiga a shafin tun da farko ya bada labarin cacar-bakin da aka yi da shi a bakin kofar shiga fadar.
Dogarawan Fadar dai sun hana shi shiga ne, saboda ya kasa nuna musu katin gayyatar sa zuwa wurin taron.
“Na dauki shawarar bada hakuri, saboda labarin da na yada da farko na ga ya janyo maganganu, don haka ina neman afuwa daga jami’an tsaro, wadanda suka hana ni shiga, domin a gaskiya dai ba su da laifi, cika-aikin da aka ba su umarni su yi suka yi.
Adeniyi ya ce Kakakin Yada Labaran Buhari, Garba Shehu ya aiko masa da katin gayyata zuwa taron wanda za a fara karfe 11 na safe, a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis.
Ya ce amma da safiyar Alhamis, sai ya samu sakon tes daga Shehu cewa an dage taron zuwa 12 na rana.
Ya kara da cewa, yayin da ya gama shirin tafiya taron, sai ya nemi katin gayyatar amma ya rasa inda ya jefa shi.
Ya aika wa Garba Shehu tes cewa ya batar da katin sa, don haka ya bar sunan sa a bakin kofa wurin jami’an tsaro, domin kada su hana shi shiga idan ya je.
Sai dai ya ce am fara samun akasi shi ne, lokacin da ya je bakin kofar, ya yi ta kiran lambar Garba Shehu, amma ta na a kashe.
“Na nuna musu katin shaida ta na dan jarida, sannan kuma na shaida musu cewa ni ne kakakin kada labaran Umaru ’Yar’Adua, Bayan wani jami’in tsaro ya tuntubi abokin aikin sa, sai ya ce na shiga cikin gidan, kuma na shiga.”
“Sai da na zo shiga dakin taro ne, abin ya faskara. Ganin haka, sai na juyo na fito daga Fadar.”
A kan hanyar Adeniyi zuwa ofis ne, sai ya aika sako a shafin sa na Twitter, cewa Garba Shehu ya gayyace taro, amma wani jami’in tsaro ya hana shi shiga, saboda bai nuna katin gayyata ba. Don haka gas hi ya na kan hanyar komawa gida dauke da buhun kunya.
Wannan sako da ya tura ha janyo da dama sun rika tofa ra’ayoyin su. Yayin da wasu ke cewa ba a yi masa daidai ba, wasu kuma cewa suke yi ai haka shi ne daidai, domin ko da a lokacin da su Adeniyi din ke mulki ne a cikin fadar, idan haka ta faru tsakanin sa da wani abokin da da ya gayyata, ba a za bar abokin ya shiga ba.
Ganin haka ne sai Adeniyi ya yanke shawarar bayar da hakuri ga jami’an tsaron.