Shugaban cibiyar ‘Child Health Advocacy Initiative, CHAI’ Lola Alonge ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tsananta sannan ta gaggauta samar da dokar hana yi wa mata kaciya a kasar nan.
Lola ta ce bayan cutuka da kaciya ke kawo wa mata, yin shi tauye musu hakki ne.
“Matan da aka yi musu kaciya na fama da matsaloli wajen haihuwa, rashin haihuwa, bayan cutuka, da dai sauran su.
Bisa ga bayannan bincike da hukumar UNICEF ta gudanar ya nuna cewa har yanzu wasu jihohi a Najeriya nan na yi wa mata kaciya. Jihohin sun hada da Legas, Osun, Ebonyi, Ekiti da Imo.
Lola ta koka ganin cewa akwai wasu kwararrun likitoci da ke aikata hakan ga mata maimakon sune za su hana abin sannan su wayar musu da kai.
Ita da wannan cibiya suna kira ga sarakuna da shugabannin addinan kasar nan dasu taimaka wajen fadakar da mutane don su gane illar dake tattare da yi wa mata kaciya.