TAMBAYA: Mata mai yi wa mijin ta asiri. Shin hakan hujja ce ga mijin ranar Kiyama.
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Sabon Allah bisa tasirin asiri ko muce sihiri. Kariya ga musulmi yana tattare da zikirin Allah da dogaro ga reshi,
duk wanda ya sabawa Allah cikin tasirin sihiri, to, ya yawaita tuba, istigfari da kyawawan ayyuka.
Amma mai sabon Allah a cikin tasirin sihiri bai da laifi ko kadan, laifin duk abinda ya aikata a cikin tasirin sihiri, yana kan wanda ya aikata masa sirihin tare da duk wanda suka bada gudun muwa cikin sihirin.
Abdullahi Dan Abbas ya ruwaito cewa Annabi SAW yace: Lallai Allah ya gafartawa al-umata laifin da suka yi cikin mantuwa da laifin da aka tursasasu akai. (Ibn Maja da Dabrani suka ruwaito)
Ya Allah! ka tsaremana Imaninmu da Mutuncinmu. Amin.