An gurfanar da Babangida Aliyu a kotu

0

An gurfanar da tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu a Babbar Kotun Tarayya da ke Minna. An gurfanar da shi ne tare da tsohon kwamishinan muhalli Umar Nasko a bisa zargin wawure kudi kusan naira bilyan biyu.

Nasko dai shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP, a zaben 2015, wanda ya sha kaye a hannun Abubakar Sani Bello na jam’iyyar APC.

Ana zargin su biyun sun karkatar da naira bilyan 1.940 daga cikin kudin raya muhalli da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar a cikin 2014.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa an dauke shari’ar ta su ce daga Babbar Kotun Taryya ta Abuja, zuwa ta Minna, babban Birnin jihar Neja a bisa ra’ayin wadanda ake karar.

Yayin da aka karanto musu tuhumomin da ake yi musu, su biyun dai ba su amsa cewa sun aikata laifin ba.

Lauya mai gabatar da kara daga EFCC, Ben Ikani, ya nemi alkali ya tsare su a kurkuku kuma ya daga karar zuwa ranar da za a fara saukaren hujjoji.

Bayan lauyan wadanda ake tuhuma ya yamutsa gashin-baki tare da lauya mai gabatar da kara, Olajide Ayodele da Mamman Osuman sun roki alkali da a ba da belin wadanda suke karewa.

A karshe alkali Yellim Bogoro ya bada belin su a kan kudi naira milyan 250 kowanen su, sai kuma masu beli mutum biyu, wadanda ma’aikatan gwamnati ne da ba su gaza ga matsayin darakta ba.

Daga nan sai alkali ya nemi su bayar da fasfo din su na fita kasashen waje, kuma ya daga shari’ar zuwa ranar 22 Ga Janairu, 2018.

Share.

game da Author