Mai Shari’a D. Z Senchi na Babbar Kotun Tarayya da ke Jabi, Abuja, ya bada belin wasu jami’an sojoji biyu da ake zargi da hannu wajen satar makudan kudade da ake ware domin biyan iyalan mamata hakkokin sojojin da suka mutu.
Wadanda ake zargin, Ishaka Yakubu da Akinbamidele Odunsi, an gurfanar da su tare da Abidemi Kolade da Violet Ofoegbunam, wadanda su biyun jami’an banki ne. Ana tuhumar su da hada baki a yi satar makudan kudade har naira milyan 399.
Wannan laifi da suka tafka, ya kauce wa dokar Najeriya Sashe na 315, a dokar 1990. An gurfanar da su ranar 9 Ga Nuwamba, inda suka ki amsa laifukan da ake tuhumar su da aikatawa, inda alkali ya tura su kurkuku har zuwa ranar 15 Ga Nuwamba domin a tattauna batun beli.
Yayin da aka koma kotu jiya Laraba, alkali ya bada belin kowanen su a kan kudi naira milyan daya kacal tare da mutane biyu da kowa zai gabatar da za su tsaya wa kowanen su.
Sannan kuma alkali ya ce kowane mai tsaya wa mai beli, ya kasance ya na da kadara a Abuja, wadda ba ta gaza darajar naira milyan 200 ba. Kuma tilas ya kawo satifiket ko takardun hakkin mallakar kadarar a ajiye a kotu.
An dage sauraron karar zuwa ranar 23 Ga Janairu, 2018.
Discussion about this post