Ni ba dan daudu bane, ni ba dan maula bane, ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi – Inji Adam Zango

2

A wata budaddiyar wasika da Adam Zango ya rubuta sannan ya saka a shafin sa na instagram ya koka da yadda ake ta yi masa zargi kan abubuwan da bai akata ba. A wasikar Adam ya ce idan har ba’a daina yi masa haka ba zai fara fadin sunayen masu yi masa haka.

Ya kuma Kalubalanci duk wanda ya ke da wata hujja cewa ya aikata abin da ake zargin sa da shi ya fito ya fadi wa duniya.

Ga wasikar:

BUDADDIYAR WASIKA IZUWA GA MAQIYANA

Ni ba dan daudu bane kuma ni ba dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi.

Da ALLAH kadai na dogara. Idan kuma akwai malamin da yace na taba zuwa wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba, toh dan girman ALLAH kada ya rufa min asiri tun daga kan yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko masu kudi, ko yammata…. duk abinda dana mallaka a rayuwata gumi na ne ya bani ba dan adam ba…motar hawa, gida ko fili….

Don haka babu wanda ya isa ya sani inyi abinda banyi niyya ba tunda babu wanda ya tayani kare mutuncin daukakata.

DON HAKA TA HANYA DAYA KADAI ZAKU IYA DAKATAR DA DAUKAKATA……HANYAR ITACE KU DAKATAR DA NUMFASHINA, SAI DAI KUMA KASH HAKAN BA’A HANNUNKU YAKE….HABA KUYI TA YAWO DANI KUNA BATA MIN SUNA DON KAWAI ALLAH YA FIFITANI AKANKU.

Kun ce min arne kunce min gay kunce min fasiki kunce min mai girman kai amma duk da haka masoyana basu gujeni ba basu daina sayan fina finai da wakokina ba. Haba don ALLAH mai nayi muku duk wanda na taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yakata!! Toh na kai bango……

Billahillazi la’ila ha illahuwa duk wanda ya kara kara tabani saina tona masa asiri. Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan abubuwan dana lissafa ALLAH ya tona masa nasa. Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma next time zan kira sunan ko waye idan ya kara bata min suna ….ina da ýaýa ya zama dole in fara kare mutuncina da martaba na kafin yayi affecting dinsu don ALLAH kadai ya san gawar fari….sannan zanja tunga da mabiyana na kannywood…. don a haka ne kadai za’a bam bance tsakanin aya da tsakuwa….

MASOYANA KU GAFARCE AKAN ABUBUWAN DANA RUBUTA, AN KURE NI NE”

Share.

game da Author