Matasan da suka cika fam na neman aiki a karkashin 2017 N-Power, za su iya binkiken sunayen su ta:
www.npower.gov.ng/npower/check.
N-Power dai ya bayyana cea a cikin 2017 za su dauki masu digiri 300,000.
Sanarwar da N-Power ta fitar, a shafin su na Facebook, an bayyana wadannan matakai kamar haka; wanda ya ke neman aiki ta N-poower zai iya bincikar sunan sa ta lambar wayarsa ko kuma lambar sirri ta asusun ajiyar ka na banki, wato BVN.
Yadda za ka binciki suna da bayanan ka a shafin N-power:
A. Ka fara shiga nan: www.npower.gov.ng
B. Ka danna inda ka ga an rubuta: ‘Check your pre-selection status’
C. Ka shiga wurin neman bayanai, wato box, sai ka rubuta suna ko adireshi ko Email or BVN
D. Idan an zabi sunan ka, zaka ga nan take sunan ka ya bayyana.
E. Za ka samu sakon tes nan take, wanda zai yi maka murna cewa an zabe ka, sauran kuma a tantance ka
F.
Daga nan z aka sai ka fara shirin tantancewa ka da za yi, ido da ido, a ranar 27 Ga Nuwamba zuwa zuwa 8 Ga Disamba, 2017