Likitoci a kasar Amurka sun gano maganin kawar da ke warkar da cutar dajin dake kama jini wato ‘Leukemia’.
Bincike ya nuna cewa mutane ‘yan shekara 7 zuwa 30 sun fi fama da wannan cutar.
Bisa ga binciken da likitocin su ka yi, sun gano magunguna biyu da ka iya warkar da cutar dajin dake kama jini mda ake kira ‘CD22’ da ‘CD19.
Likitocin sun ce sun gwada magungunan a jikin mutane 21 da ke dauke da cutar ‘yan shekara 7 zuwa 30.
Koda suka yi hakan babu wanda ya sami sauki daga cikin mutanen. Amma da suka hada magungunan waje daya suka gwada a jikin mara lafiya sai yayi aiki.
An gwada maganin a jikin mutane 15, 11 sun warke.
Yanzu za a hada magungunan waje daya domin yin amfani da shi.