Artabu ya kacame tsakanin EFCC, SSS da NIA a Asokoro

0

A yan zu haka lokacin da ake rubuta wannan labari, jami’an Hukumar EFCC na can na artabu da jami’an tsaro na SSS da kuma na NIA.

EFCC dai ta kai sameme ne a gidajen tsoffin shugabannin SSS da NIA, domin su kama su. Amma sai dakarun da ke tsaron su suka hana a tafi da su.

A na can ana cukumurda a kan titin Justice Mamman Nasir, da ke cikin unguwar Asokoro, Abuja, inda gidajen tsohon shugaban NIA Ayo Oke da na SSS, Ita Ekpoeyong suke.

An hana motoci wucewa ta kan titin, wanda hakan ya sa unguwar Asokoro ta yi cancak da dandazon motoci.

Share.

game da Author