Muna nan akan bakan mu na koran malaman da suka fadi jarabawa – El-Rufai

2

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin sa na nan akan bakanta na koran malaman da basu ci kashi 75 bisa 100 na gwajin da akayi wa malaman firamaren jihar ba.

El-Rufai ya rubuta matsayin gwamnatin sa ne a shafin sa na sada zumunta ‘Facebook’ in da ya kara da cewa ba zasu yi amai su lashe ba.

” Mun sami sakon kungiyar malamai ‘NUT’ cewa wai zasu fara yajin aiki na bai daya daga ranar 23 ga watan Nuwamba, amma abinda muke so su sani shine basu da wata dalilin yin hakan.”

” Mun dauki alkawarin cewa za mu yi wa mutane aiki. Mun yi rantsuwa akan haka, kun ga ko ba za mu saba alkawari ba don suna bamu tsoro da yajin aiki.”

El-Rufai yace wannan abu anyi don ‘ya’yan talakawa ne saboda haka ‘NUT’ baza su ba gwamnatin sa tsoro ba.

” Muna nan akan bakan mu na koran duk wadanda basu ci jarabawar ba sannan zamu dauki kwararru, wanda mun riga mun fara.”

Share.

game da Author

  • Aminu Muhammad Baba

    Ka yi dai dai gwamnan al’ummar Kaduna. Sun yi shekara da shekaru suna gurbata ilimin yara wajen sakaci da inspection, da refresher courses da continuous assessment na malamai da shirya rashin gaskiya wajen daukar wayanda suka cancanta domin basu da gālihu sai a bar su a dauki masu gata. To yanzu me gyara yazo saboda bamu da tsoron Allah mun fara kushe masa. El-Rufai in dai domin Allah kake yi to bar Shi da mutane marasa godiya, Allah na tare da kai. ولله يعصمك من الناس
    Domin shi dan Adam, musamman ma dan Adam din Najeriya, babu abinda zai cika masa ciki sai Qasar Kabari

  • Kabiru musa

    Yakamata gwamna yasake nazari akan kudirinsa na koran maluman nan. Domin aiwatar da wannan kudiri zai shigar da magidanta da iyalansu dayawa cikin halin kakani kayi da rudani