Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko Faisal Shuaib ya ce za su fara yin alluran rigakafin cutar Bakon Dauro a Kaduna.
Za a fara yin alluran daga yau Talata, 7 ga watan Nuwamba 2017. Faisal ya ce za a yi wa yara miliyan 33. Bayan haka kuma karamin ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ne zai kaddamar da yin alluran ga yara ‘yan watanni 59 zuwa shekara 9.
Ya kuma kara da cewa babbar burin su shine su yi wa kashi 95 bisa 100 na yaran kasan alluran rigakafin cutar a shekaran a wannan karon.
Bayan haka ya yi kira ga iyaye da suyi amfani da wannan dama su turo ‘ya’yan su domin yin allurar da zaran an fara yi a jihar da kasa baki daya.
Faisal ya ce za su kafa wuraren yin alluran rigakafi a makarantu, asibitoci, tashoshin mota, masalatai, coci sannan za a bi gida gida domi yi wa wadanda suke gida.
Ana sa ran gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai na daga cikin manyan bakin da zasu halarci kaddamar da yin allurar.