An samu Gwamnan Babban Bankin Nijeriya dumu-dumu da hannu cikin harkallar kafa kamfanoni a kasashen waje domin karkatar da kudaden da ake gudu gwamnati ta san da zaman su, harkallar da ‘Paradise Papers’ su ka fallasa a ranar Lahadi da ta gabata.
An samu sunayen Emefile a cikin kamfanoni uku, wadanda shi da kan sa ya taba tabbatar da cewa ya na cikin daya daga cikin su a Yuli, 20017, yayin da ya na kan mukamin sa na gwamnan CBN.
Binciken da PREMIUM TIMES ta yi ita da gamayyar kungiyar zaratan ‘yan jarida masu binciken kwakwaf na duniya, wato ICIJ, ya tabbatar da haka.
Emefile na daya daga cikin masu kamfanin Vitesse Asset Management SA, wanda aka yi wa rajista cikin 2007; kuma shi ke da Oviation Management Limited, wani kamfani da ke Bermuda, wanda ya kafa cikin 2009; sai Oviation Limited, aka yi masa rajista cikin 2012. Haka dai bincike ya tabbatar wanda jaridar Jamus mai suna Suddeutsche Zeitung ita ma ta fallasa.
Baya ga wannan karmaya-karmayar, wasu bayanai sun sake tabbatar da cewa Emefile tare da shugaban bankin Zenith, Jim Ovia sun mallaki wasu kamfanoni karkashin Shell. Kada a manta, kafin Emefile ya zama shugaban CBN, ya yi aiki a karkashin Ovia a Bankin Zenith. Shi ne mataimakin sa a lokacin da shi Ovia ya ke rike da mukamin Manajan Daraktan Zenith. Ya zama shugaban CBN ranar 3 Ga Yuni, 2014.
Takardun bayanan da PREMIUM TIMES ta bankado, sun nuna cewa Emefile na da hannun jari har guda 50,000 a kamfanin Vitasse Asset Management, sannan kuma shi ke da kashi 100 na hannun jarin Oviation Limited.
Wasu bayanai kuma sun nuna Shell ya na hada-hadar jiragen sama na alfarma ne, sannan kuma ya na safarar makudan kudaden kasashen waje a wani tsari na sirrin da su ke kauce wa biyan haraji.
Wannan kamfanoni ba su da ofis, babu ma’aikata ko daya, ba su ma da kwamfutoci ballantana layukan adireshi na lambar tarho a dukkan kasashen da aka ce su ke hada-hada. Ana dai ganin su na kimshe kadarori a tsakanin su, tare da bayar da lamunin milyoyin daloli a tsakanin su, a cikin wani yanayi mai sakala-sakala.
An yi hada-hada mai tarin yawa a karkashin Oviation Asset Management Limited. Misali, cikin Yuli, 2011, kamfanin ya sayo jirgin sama samfurin Jet a kan kudi Dala milyan 12,755,000 daga wani kamfani mai suna Churchill Finances, wanda shi kuma wani kamfani ne na kasar waje, mallakar Sayyu Dantata, shugaban kamfanin MRS Oil Nigeria Limited.
Amma bayan shekara biyu aka saida jirgin ga wani kamfanin su, inda su ka yi ikirarin faduwa har ta asarar dala miliyan 1.3.