Mafarauta dake kauyen Gur, jihar Barno, da na garin Damaturu, jihar Yobe sun kashe daya daga cikin ‘yan Boko Haram kuma barayin shano a dazukan yanki.
Kakakin rundunar sojin Najeriya,Janar Sani Usman ya ce tuni an mika dabbobin ga jami’an tsaro domin yin bincike da mika wa masu wadannan dabbobi abin su.