ATIKU: Ra’ayin sa ne ficewa daga APC – Jam’iyyar APC

0

Jam’iyyar APC ta ce ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daga APC ba wani abu bane illar yin abin da yaga ya dace masa.

Kakakin jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi ne ya sanar da mana da haka ta wayar tarho, da muka nemi ji ta bakin jam’iyyar.

“ Idan yana ganain a wata jam’iyyar ne zai iya cimma burin sa a siyasa, yana da ikon yin hakan. Sai fa lalli mun rasa wani jigo amma hakan ne yake ganin ya fi masa. Mun rasa wasu ‘yan siyasa amma kuma mun samu wasu suna shigowa jam’iyyar. Duk da haka za mu dubu domin gyara inda akwai matsala.” Inji Bolaji Abdullahi.

Share.

game da Author