Kemi ta dakatar da shugaban ‘SEC’ Munir Gwarzo

0

Ministan Kudi Kemi Adeosun ta dakatar da shugaban hukumar ‘Security and Exchange Commission’ Munir Gwarzo.

Ma’aikatar ‘SEC’ dai ma’aikata ce da ke karkashin ma’aikatar kudi na kasa.

Kemi ta ce an dakatar da Gwarzo ne saboda zargin harkallar kudi a ake masa ya aikata a ma’aikatar ‘SEC’ din.

Bayan haka kuma ta sanar da kafa kwamiti da zai binciki wannan harkalla. Bayan shi an dakatar da wasu manyan daraktoci a hukumar, Abdulsalam Naif Habu, da Anastasia Omozele Braimoh wanda suma a na zargin su da hannu a harkallar.

Share.

game da Author