Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta sanar da kisan gilla da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Daktibe Jaligo dake jihar Gombe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Shina Olukolu ya sanar da haka wa manema labarai yau Laraba inda ya ce ‘yan bindigan sun kashe mai unguwan kauyen Adamu Garba tare da dansa Muhammed.
Olukolu ya ce tuni sun fara gudanar da bincike akai don ganin sun kamo wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.
Wani basarake, Tula Abubakar Buba ya yi kira ga gwamantin tarayya da jami’an tsaro da su kara matsawa wajen ganin an samar da tsaro a yankin da kuma kamo wadannan mutane.
Bayan kashe mai unguwar garin da dan sa da suka yi, matar sa da sauran ‘ya’yan sa sun sami raunuka sanadiyyar harin. Suna asibiti ana kula da su.