An sako ma’aikacin jinyar da aka sace a Gombe

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe Shina Olukolu ya sanar da cewa an sako ma’aikacin jinya Ephraim Ajuji da wasu mautane suka sace ranar Talata a Dadin- Kowa.

An yi garkuwa da Ephraim ne ranar litinin din daya gabata.

Diyar Ephraim, Mary Ephraim da ita ma ta tsira da sara a kanta ta fadi wa manema labarai cewa barayin sun sace mahaifinta ne da misalin karfe 7 na safen Talata.

‘‘Barayin sun bukaci a biya su Naira miliyan 10 kafin su sake shi ko kuma su kashe shi idan ba mu biya kudin ba’’.

Daga karshe Olukolu yace saboda kokari da jami’an tsaro suka yi masu garkuwan sun sako Ephraim.

Share.

game da Author