Kwana daya bayan fallasa wani labari da Shugabar Ma’aikata ta bayyana cewa da sanin Shugaba Muhammadu Buhari aka sake mayar da Abdulrashid Maina a kan aiki, har yanzu Fadar Shugaban Kasa ba ta ce komai ba.
An dai fallasa wata takardar sirri ce wacce Shugabar Ma’aikata, Winifred Oyo-ita, ta bayyana a rubuce cewa da sanin Buhari aka yi rikita-rikitar maida Maina bakin aikin sa.
“Saboda na nemi ganin Shugaban Kasa a ranar 11 Ga Oktoba, 2017, bayan taron Mazalisar Zartaswa, inda na bayyana masa baki-da-baki illar maida A. A Maina a bakin aikin sa, musamman yadda abin zai taba sahihancin yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnatin ke yi.” Haka Oyo-Ita ta zayyana a cikin wasikar da ta aika wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.
Jaridu biyu, PUNCH da Sahara Reporters sun buga wayanan da su ka kara tabbatar da cewa Buhari na da masaniyar yadda aka yi karmaya-karmayar maida Maina kan aikin sa.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ce jaridar da ta fara fallasa labarin yadda aka yi sunkurun shigo da Maina cikin Nijeriya daga gudun hijirar da ya ke yi, kuma aka maida shi kan aikin sa.
Wannan labari dai ya janyo wa gwamnati bakin jini tare da tofin Allah wadai. PREMIUM TIMES ta kuma fallasa yadda Ministan Shari;a Abubakar Malami da kuma Ministan Harkokin Cikin Gida Abdulrahman Dambazau su ka yi kitimirmirar dawo da Maina.
Dukkan kiraye-kirayen da jama’a su ka rika yi suna cewa Shugaban Kasa ya tsige Dambazaau da Malami, sun bi ta bayan kunnen Buhari, har yau bai ce komai ba.
Ba mamaki wasikar da Oyo-Ita ta rubuta, an aika ta ne sakamakon Buhari ya nemi cewa babban jami’i ya rubuta bayanin yadda aka yi aka maida Maina bakin aikin sa a asirce.
TAMBAYOYIN DA HAR YAU BABU AMSA
Duk da cewa an fallasa yadda Oyo-Ita a matsayin ta na Shugabar Ma’aikata ta rubuta cewa Buhari na sane da dawo da Maina a asirce, akwai tambayoyin da ke bukatar amsa, amma har yau babu.
Misali, ba a ji martanin da Buhari ya maida wa Oyo-Ita ba, yayin da ta bayyana masa cewa dawo da Maina fa babbar matsala ce. Shin Buhari cewa ya yi umarnin a dakatar da Maina, ko kuwa cewa ya yi a bar shi ba komai?
Oyo-Ita ta fada a cikin wasikar ta, cewa tun cikin watan Fabrairu ta fara jinn kishin-kishin din za a maida Maina bakin sa. Amma me ya sa ba ta sanar wa Shugaban Kasa ba?
Me ya sa ta yi tattaki ta yi wa Buhari bayanin Maina baki da baki, maimakon ta yi abin da ka’ida ta ce, wato ta rubuta wasika?
Kada a manta, PREMIUM TIMES ta fallasa labarin komawar Maina bakin aiki, kwanaki 9 bayan Oyo-Ita ta yi wa Buhari bayanin dawo da shi.
Me ya hana a cire shi a cikin wadannan kwanakin?
Discussion about this post