Mutane 50 ne suka rasa rayukan su a harin Mubi – Rundunar ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sanar cewa mutane 50 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar bam din da wani dan kunar bakin wake ya tada a wani masallaci daki unguwan Shuwa, karamar hukumar Mubi ta arewa.

Jami’in harka da jama’a na rundunar Othman Abubakar ya tabbatar da haka da yake zantawa da manema labarai.

Abubakar ya ce har yanzu ba a san yawan mutanen da suka sami raunuka a harin ba amma sun sami tabbacin mutuwar mutane 50 a harin.

Shi ko shugaban karamar hukumar Mubi ta arewa Musa Bello ya ce har yanzu basu da ainihin lissafin yawan mutanen da suka rasu a harin.

Wani matashi dauke da bam ne ya tada ta a wani masallaci, daidai ana sallar asuba. An kiyasta shekarun sa kan 17.

Hukumar bada agajin gaggawa NEMA a jihar ta ce duk wadanda suka sami raunuka suna samun kula a wasu asibitoci dake garin Mubi.

Share.

game da Author