A ci gaba da ajiye Maryam Sanda a Kurkuku – Kotu

0

Kotun dake sauraren karar da rundunar ‘yan sandan Abuja ta shigar kan yarinyar nan da ta kashe mijinta ta yanke hukuncin cewa a ci gaba da ajiye Maryam a Kurkuku zuwa ranar 7 ga watan Disamba.

Kotu tayi watsi da kiran da lauyan Maryam yayi na aba ta Beli.

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja ta shigar da kara babban kotun tarayya dake Abuja tana neman a yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa saboda kashe mijin ta Bilyaminu Bello Halliru da tayi.

Ana zargin Maryam Sanda da daba wa mijin ta Bilyaminu fasasshen kwalba da niyyar kashe shi.

Bayan aikata haka, Bilyaminu ya rasu sanadiyyar wannan sara.

‘Yan sanda sun ce wannan abu ya faru ne a gidan su da ke unguwan Wuse, Zone 2 ba Maitama ba kamar yadda ake ta yadawa.

Share.

game da Author