Muna jiran PDP ta tsayar da ATIKU, ya zo mu fafata a filin daga, Zan yi barci na har da munshari – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce dama can sun sani cewa tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar zai fice daga jam’iyyar APC a watan Disamba ba ne sai gashi ya fice a watan Nuwamba. Hakan kuma ya yi mana dadi domin gara da ya tafi tun yanzu.

El-Rufai ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da aka tambaye shi ko mai zai ce kan ficewar Atiku daga jam’iyyar APC.

“ Ko lokacin da na rubuta wa shugaban kasa wasika, na yi masa magana kan jawo wasu yan jam’iyyar kusa dashi da ya hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Sauran da na Ambato duk susna nan ana tafiya dasu amma shi ya ki.

“ Sannan ina so in sanar muku cewa babu wani gwamnan jam’iyyar APC da zai tafi tare dashi. Dama can gwamnan Adamawa ne idan ma z aka ce akwai daya, amma kuma shi ma din bai dade ba y ace yana tare da Buhari 100 bisa 100.

“ Sannan na gaya masa tun a 2014 da muka hadu a Dubai cewa kada ya ja da Buhari, Buhari Ikon Allah ne kuma wannan lokacin sa. Amma yaki ji. Haka ma duk wani dan Arewa da yake ganin zai iya, ya hakura kawai domin yanzu lokacin Buhari ne. Muna nan muna jira PDP ta bashi tiket, yazo mu fafata. Ina tabbatar muku b azan rasa barci na ko na sakan guda ne ba idan dai yafito takara da Buhari.

Share.

game da Author