Wadanda suka cika fam domin neman dauka aiki a tsarin N-Power za su fara karakainar kokarin tantance sui do-da-ido.
Haka dai hukumar gudamanarwar Shirin N-Power ta bayyana.
Bayanin da suka buga a shafin su na Facebook, ya nuna cewa za a fara tantancewa ido-da-ido kafin a dauki na dauka a tsakanin 4 zuwa 14 Ga Disamba, 2017.
Daga nan sai aka fitar da yadda aka bi har aka zabi wadanda za a tantance din, bayan da wadanda bas u yi nasara ba su ka fara korafi da neman jin ba’asin yadda aka ki tantance su.
Tsarin N-Power dai wani shiri ne da gwamnatin tarayya ke bayar da tallafi a karkashin shirin rage radadin talauci, wato, Social Intervention Programmes, wanda aka tsara daukar marasa aikin da suka kammala digiri. Za a dauki 300,000 a cikin 2017.
MANUNIYA: Duk wanda ya cike fam amma har yanzu bai san matsayin da ya ke a ciki ba har yanzu, to sai ya bi wadannan hanyoyi uku da ke kasa domin ya san shin ya na cikin wadanda za a tantance din ko a’a.
Ka shiga shafin N-Power na intanet, mai Suna: www.npower.gov.ng
2. Sai ka latsa inda aka rubuta “check your pre-selection status”.
3. Sai ka rubuta sunan ka, ko lambar wayar ka ko adireshin ka ko lambar ka ta BVN.