Za mu tattara na-i-na mu bar Jihar Benue saboda sabon dokar kiwo – Fulani

0

Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah reshen jihar Benue MACBAN ta ce makiyayan jihar za su tattara nasu- i-nasu su fice daga jihar ganin cewa ba za su iya cika sharuddan da gwamnati ta gindaya musu wanda ciki harda siyan filin kiwo kafin 1 ga watan Nuwamba ba.

Shugaban kungiyar Garus Gololo ya fadi haka da yake zantawa da kamfani dillancin labaran Najeriya ranar Talata a Makurdi inda ya kara da cewa barin jihar ya zama musu dole ganin cewa gwamnatin jihar ta matsa sai ta tabbatar da dokar hana kiwo a jihar.

Gololo ya ce duk da sun yi ta jira su ga ko za a samar musu da wuraren kiwo da siyar da dabbobin su amma ba ayi haka ba gashi dokar zai fara aiki ne daga 1 ga watan Nuwamba.

“Cikin sharuddan da aka bamu na zama a garin shine mu nemi wurin zama wato mu siya filaye kenan amma kowa ya sani cewa siyan fili daga wurin gwamnati nada matukar wahala balle kuma samun takardun shaidar siyan filin ( Certificate of Occupancy).”

“Sun ce sun tsara dokar ba don kare mana hakkin mu bane saboda lokacin da suka ba mu don cika wadannan sharudda sun yi kadan wanda hakan ya sa muka yanke shawaran barin garin kawai.”

Gololo ya ce duk sun roki gwamnatin jihar da ta kara basu lokaci amma ta kafe a kan tsarinta.

Bayan haka kwamishinan yada labarai Lawrence Onoja Jr. yace tsawon kwanakin da aka bawa makiyayan ya ishe su su sami filayen zama.

” Mun samar da duk abin da zasu bukata da ya shafi doka wanda zai sauwake musu mallakar filin kiwo amma suki bi sabo da haka dokar hana kiwo na nan 1 ga watan Nuwamba. Duk wanda bazai iya bin dokara ba ya bar jihar.”

Share.

game da Author