RANAR POLIO: Shekara uku kenan ba a sami bullowar cutar Polio a jihar Yobe ba

0

Shugaban hukumr kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Yobe Hauwa Goni ta ce bana sun yi wa yara ‘yan kasa da shekara biyar alluran rigakafin cutar shan inna miliyan 1.1 a jihar.

Ta sanar da haka ne a tattaki da akayi a Damaturu domin ranar Polio na duniya.

Hauwa Goni ta kara da cewa jihar ta yi shekara uku kenan ba a samu bullowar cutar shan inna a ko-ina a jihar.

Goni ta ce suna kokarin hada karfi da karfe da fannin ilimi na jihar,addini da sarakunan gargajiya don wayar wa mutane kai kan mahimmacin yi wa yara alluran rigakafi.

Share.

game da Author