Shin ko kasan cewa shi man gyada sau daya kawai ake so ayi amfani da shi kuwa? Shi man gyada ya kan zama abin gudu muddun an riga an yi amfani dashi domin yana kara wa mutum kiba ne sosai.
Masana sun bada shawara cewa idan har mutum sai yayi amfani da man gyada, to ya dibi daidai yadda zai yi amfani dashi kada ya rage mishi, domin wanda ya rage kuma a ka sake amfani dashi ne ke sa kiba a jiki.
Wata likita mai suna Katlyn Okrowafor ta yi kira ga mutane musamman masu kiba da su mai da hankali wajen irin abincin da suke ci saboda lafiyar jikinsu. Bayan haka kuma ta bada shawara kan wasu hanyoyi da za abi don guje wa fadawa irin wannan matsala na kiba da wasu cututtuka da zai iya kama mutum idan ya yi irin wannan kiba.
Katlyn Okrowafor ta shawarci mutane da su guji cin abinci latti musamman da daddare. Idan har ya zama dole sai anci to, aci cin kayan lambu ne kawai.
Likitan ta bayyana irin abincin da mutum zai iya kiyayewa domin guje wa kiba kamar haka;
1. Buredi: Yawan cin buredi na kawo kiba a jiki musamman idan aka ci da daddare sannan idan mutum na da kiba kamata yayi a rage cin sa domin yawan cin sa kara kiba yake yi.
2. Yawan cin abincin da aka soya kamar su dankali, doya, cin-cin, da sauran su na kara kiba a jiki.
3. A rage amfani da man gyada wajen girki musamman idan an yi amfani da man wajen soya wani abu kamar nama ko doya.
Ta ce amfani da irin wannan man bashi da kyau domin kiba yake karawa mutum kawai a jiki saboda duk sauran sinadarin da ke ciki kamar ‘Vitamin A’ ya kone.
4. A rage shan giya domin banda kiban da yake karawa yana kuma kawo cutar siga.
5. A rage cin kitse.