Tsutsar ciki na daga cikin ababen da ke hana yara girma a Najeriya

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga iyaye da su dinga amfanin da maganin kawar da tsutsan ciki wa yaran su domin bunkasa kiwon lafiyar ya’yan.

Kungiyar WHO ta ce bincike ya nuna cewa yara biliyan 1.5 na fama da matsalolin rashin kuzari da girman jiki sanadiyyar tsutsan ciki.

Kungiyar ta ce matsalolin da ya hada da rashin tsaftatace muhalli da ruwan sha na cikin kalubalen da ke kawo cutar tsutsan ciki musamman ga yara kanana.

Wani jami’in kungiyar WHO Dirk Engels ya kara da cewa saboda hakan ne kungiyar ke kokarin wayar da kan mutane kan mahimmancin zama cikin tsaftatacen muhalli, shan da tsaftacacen ruwan sha da kuma shan maganin tsutsan ciki akalla sau biyu a shekara domin hakan zai bunkasa girman jikin yaro.

“Muna sa ran cewa shirin zai taimaka wajen kawar da cutar tsusan ciki a jikin kashi 75 bisa 100 daga cikin yara 875 da ke fama da cutar daga nan har zuwa 2020.”

Share.

game da Author