Kungiyar kwadugo NLC reshen jihar Benue ta shiga yajin aiki yau Talata 3 ga watan Oktoba.
Shugaban kungiyar Godwin Anya ya ce kungiyar ta shiga yajin aikin ne saboda rashin cika alkawuran da gwamnatin jihar ta dauka na biyan bukatun ma’aikata da ya hada da biyan albashin su da biyan kudaden fansho na ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar.
Ya ce yayin da suke tattaunawa da gwamantin jihar kungiyar NLC ta ture tayin biyan albashin ma’aikata na wata biyu da gwamnatin jihar ta yi mata.
“Kamata ya yi ace gwamnati ta biya duk albashin watanni biyar din da ma’aikata ke binta ba wai ta ce za ta biya su na wata biyu ba.”
Godwin Anya ya ce za su ci gaba da yajin aikin har sai gwamnatin jihar ta biya duk bukatun su.