Mai Shari’a John Tsoho da ke Babbar Kotun Birnin Tarayya, ya janye kan sa daga shari’ar wasu ‘yan Boko Haram su takwas da aka gurfanar a kotun sa.
Ya yanke wannan shawara ce a ranar Laraba, yayin da wasu shida daga cikin wadanda ake tuhumar su ka nemi kotun da dauke shari’ar daga karskashin kotun sa zuwa wata kotun.
Su dai wadanda ake tuhum din, su na fuskantar shari’a ne a Babbar Kotun da ke Abuja, dangane da hannun da su ke da shi wajen kisan wasu ‘yan kasar waje su biyar da suka sace, kuma su ka yi garkuwa da su kafin su kashe su. Kisan ya faru ne a cikin jihar Krbbi, cikin 2011.
Ana kuma zarginsu da kashe wasu ‘yan kasar waje bakwai a jihar Barno, wadanda su ka arce da su daga cikin jihar Bauchi a watan Fabrairu, 2013, su ka tafi da su har cikin Dajin Sambisa su ka kashe.