Bi-ta-da-kulli Buhari ke min, ba bincike ba -Patience Jonathan

0

Uwargidan tsohon shugaban kasa Gooodluck Jonathan, Patience, ta ce binciken da ake yi mata ya na da nasaba ne da rawar da ta taka wajen taya mijin ta yakin neman zaben 2015.

Patience, wadda ta amince cewa ita ce ke da wasu zunzurutun makudan kudaden da hukumar EFCC ta rike har dala miliyan 15.5, ta bayyana wannan zargi na bi-ta-da-kulli ne jiya Litinin a cikin wata takarda da mai taimaka mata a harkar yada labarai, Belema Meshack-Hart ya sa wa hannu.

Daga nan sai ta roki Shugaba Buhari ya rika mutunta ta kamar yadda ya ke mutunta uwargidan marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’Adua, wato Turai.

“Mun yi imani ana kuntata wa Patience ne saboda tsantsar goyon bayan da ta bai wa mijin ta yayin yakin neman zaben 2015.

“Shugaban Kasa ya tuna shi ma ai matar sa ta fito ta nuna masa goyon baya ta na caccakar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Amma shi Jonathan bai bi matar Buhari da ramauwar gayya ba.

Ta ce idan dai akwai mutunci, to bai kamata a yi amfani da dalilin abubuwan da su ka faru a lokacin zabe ba, a rika gallaza mata, har ana yi mata bi-ta-da-kulli, wai dukan kabarin kishiya. Ta mutu, ba a bar gawar ta ta sarara ba.

Sai kuma ta ja hankalin shugaban EFCC Ibrahim Magu da ya daina shige mata hanci da kudundune.

Patience ta kuma yi kira ga Buhari da ya dauki darasi daga Amurka, inda tun da Donald Trump ya hau mulki, bai sake komawa kan uwargidan Obama, Michelle ba, duk kuwa da irin caccakar da ta yi masa a lokacin kamfen.

“Duk kasashen da ake tafiya kan turbar dimokradiyya a duniya, matan shugabanni kan taya mazan su kamfen. Mun ga haka a Amurka, amma Trump bai rika cin dunduniyar Michelle ba. Amma dai magana daya a nan ita ce, duk irin matsin-lamba da kuntatawar da za su yi wa matar Jonathan, to za ta ci gaba da mara wa mijin ta baya a duk kowane irin rintsi ya samu kan sa a ciki. Tunda kuma shi ne uban ‘yan’yan ta, kai ko da za ta rasa ran ta, ba za ta kware wa mijin ta ba ya ba.”

Share.

game da Author