Rashin adalci ne kowane yanki ya samu yawan jihohi daidai da saura, inji El-Rufai

0

Shugaban Kwamitin Tattauna Fasalin Najeriya na Gwamnonin APC, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bukatun da wasu ke nema na a kirkiro yawan jihohi a kowace shiyya daidai da kowace, rashin adalci ne.

Ya yi wannan bayani jiya Laraba, yayin da ya ke tattaunawa da wasu matasa a Abuja.

Yanzu dai a Najeriya yankuna hudu daga na da jihohi shida kowanen su, yayin da Arewa maso yamma na da jihohi bakwai, Kudu maso gabas na da biyar.

“Ba za ka zo ka ce mu kirkiro jihohi tara a kowane yanki ba, saboda yawan al’umma, fadin kasa da kuma yawan albarkatun kasa na kowane yanki ya sha bamban da na sauran yankuna. Bai yiwuwa ka maida abubuwan da ba daidai su ke ba, su zamo daidai da juna.

Sannan ya kara da cewa bai yiwuwa jihar da ke neman ta rika sarrafa kashi 100 na albakatun ta, ta samu wannan damar kashi 100 bisa 100.

A tasa fahimtar, jihohin da ba su da arzikin danyen mai sun fi yawa, don haka masu danyen mai ba za su samu yawan kuri’un da su k enema ba a Majalisar Tarayya. Domin Majalisar Tarayya ce kadai za ta iya amincewa da abin da su ke nema, ba kuma za su amince ba.

“Don haka ya kamata dai a fara neman abin da aka san zai amfani kasa baki daya, ba wai a rika neman abin da kawai zai amfani wasu tsiraru ba.”

Ya ce kudin da ake bai wa jihar Kaduna domin gudanar da tsaro, ba a hannun sa su ke ba, Sakataren Gwamnatin Jihar ne ke kula da su, kuma a shirye ya ke ya bayar da litttafin da ake rubuta abubuwan da aka yi da kudaden domin mai bukata ya gani da idon sa.

El-Rufai ya ce masu cewa a soke tsarin Majalisar Dattawa a Najeriya, hakan ba zai taba yiwuwa ba, domin Majalisar Dattawan ce da kan ta kadai za ta kada kuri’ar neman ta rushe kan ta. Kenan ya ce babu wanda zai yarda ya kada kuri’ar rushe kan sa.

“Masu cewa a kara kirkiro jihohi, a gefe daya kuma su na cewa kudin da ake kashewa wajen tafiyar da sha’anin gwamnati sun yi yawa sosai, to kun ga su na tubka kuma su na warwarewa da kan su kenan.

Ranar Juma’r da ta gabata Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Ike Ekweremadu, ya bayyana cewa sun karbi bukatu har guda 45 daga masu bukatar a kara kirkiro wasu jihohi daga cikin 36 da mu ke da su a halin yanzu.

Share.

game da Author