Bayan sanarwan da gwamnan jihar Kaduna yayi cewa da yawa daga cikin malaman makarantun firamaren Kaduna basu cancanci koyar da daliban makarantun ba in da hakan ya jawo cecekuce da ya sa har kungiyar Kwadagon NLC a jihar ta fito ta musanta gwamnan jihar.
Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar wa wakilan bankin duniya da suka ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar cewa cikin malamai 33,000 da suke karantarwa a makarantun jihar, 20,000 basu ci jarabawar da gwamnatin jihar ta shirya musu domin gane kokarinsu wajen karantar da yaran da ke makarantun ba.
Jin haka ke da wuya ita kuma kungiyar kwadagon jihar ta fito ta soki wannan magana da gwamnan yayi in da tace El-Rufai ya yi haka ne don neman suna kawai amma ba wai don ya na fadin gaskiya ba.
Bincike da muka gudanar akan hakan ya nuna mana cewa lallai gwamna El-Rufai na da gaskiya game da abin da ya fadi wa bakin sa.
Wani shugaban makarantar firamare da baya so a fadi sunan sa ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa a makarantar sa kawai kusan duka malaman da suke karantar da dalibai basu cancanci hakan ba idn gaskiya za abi.
“ Ina Hedimasta ne a makarantar gwamnati a jihar Kaduna kuma ni da sauran duk wani shugaba da zai fadi gaskiya akan aikinsa ya san gwamnan ya fadi gaskiya ne. Kusan duka malaman makarantun da za a gani ba wai cancanta bane suke dashi, an dauke su ne kawai don siyasa. Wata ma a makarantar take koyan yadda za ta yi rubutun kirki amma kuma wai malama ko malami ne.”
Wata malama, Samira Lawal da ta zanta da wakilin mu ta ce idan har za a yi wa gwamnan adalci, gaskiya yana kokarin gyara fannin ilimi ne a jihar kuma korafin da yayi akan malaman gaskiya ne.
“ A gaskiya ko mu muna gani a makarantun da muke karantar da yara. Za ka ga malama ba ta iya karatu ba amma wai tana karanta da dalibai. Sannan maganan jarabawa da akayi tabbas su kansu malaman da suka rubuta da yawa suna kuka cewa basu san me za su rubuta ba wajen amsa tambayoyin.”
Mutanen jihar da suka tattauna da wakilin mu sun roki gwamnan da kada ya karaya da babatun da NLC sukayi akan abin da yace game da malaman jihar. Sun roke shi da ya ci gaba da aikin gyara makarantun jihar.
“ Duk wani makarantan gwamnati da ka gani ‘ya’yan talakawa ne ke karatu a cikinsu shi. Duk wadanda suke magana ba a irin wadannan makarantu ‘ya’yansu suke ba. El-Rufai ya na so ya gyara su kuma suna so su mai da abin siyasa.”