Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa wasika, ya na mai neman amincewar su da Aisha Ahmed a matsayin Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ne ya karanta wasikar a zauren Majalisar yau Alhamin, inda aka nuna cewa amincewar ta zama dole ganin cewa wadda aka aika musu da sunan nata, za ta maye gurbin daya daga cikin mataimakan gwamnan ne, wanda ya yi ritaya tun farkon wannan shekara.
Bayan Aisha, Buhari ya kuma nemi Majalisar da ta amince da sunayen wasu mutane hudu wadanda aka aika musu, a matsayin mambobin kwamitin sa-ido a harkokin babban bankin na kasa, CBN. Su ma hudun za su maye gurabun wasu mambobin guda hudu ne, wadanda za su kammala wa’adin su a karshen wannan shekarar.
Sunayen da Buhari ya aika na mambobin kwamitin sun hada da: Adeola Adenikiju, Aliyu Sanusi, Robert Asogwa da Asheik Maiduguri.