RANAR POLIO: Shekara biyar kenan ba Polio a Kaduna

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar cewa shekara biyar kenan ba a sami bullowar cutar Polio a ko ina a jihar ba.

Shugaban ma’aikatar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko Hadiza Balarabe ne ta fadi haka a Kaduna wajen tattaki da akayi a jihar domin ranar Polio na duniya.

Ta ce tun a watan Disembar 2012 ba a sake samun labarin cutar ba a jihar Kaduna. Ta yi kira ga ‘yan jihar da su ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya don ganin hakan ya dore.

Hamza Ikara, ne ya wakilci shugaban hukumar a tattakin.

Share.

game da Author