Dalilan da ya sa na Kafa gidauniyar ‘Todays Life Foundation’ – Mansurah Isah

0

A hira da PREMIUM TIMES tayi da mansura Isah, ta zayyano wasu dalilai da yasa ta kafa gidauniyar ‘ ‘Todays life Foundation’.

Mansura ta ce tausayi da ganin halin da wasu mutane ke shiga ne musamman abin da ya shafi rashin abin da za su ci ma kawai yasa ta kafa gidauniyar don ita ma ta bada nata gudunmuwar sannan kuma tallafawa yara da ke gararamba a titunan mu ta hanyar taimakawa iyayen su da su kansu a sa su makaranta.

“ Ita wannan gidauniya na kafa ta ne don taimakawa marasa karfi, matan da suka rasa mazajen su da kuma yara kanana. Na yi haka ne domin bada gudunmuwa ta ga mutane da ke cikin halin kakanikayi.

Mansura ta ce gidauniyar ta na samun kudaden ta ne ta hanyar tallafi da kyauta da ta ke samu.

“ Gidauniyar ‘Todays Life Foundation’ na samun kudadenta ne ta hanyar tallafi da kyauta daga ‘yan uwa da abokan arziki. Sannan kuma mijina ma ya na mara mini baya akan haka.”

Jarumar ta ce wannan gidauniya na ta zai ci gaba da taimakawa talakawa da marasa galihu ba a Kano ba kwai har ma da wasu jihohin kasar nan.

“ Yanzu haka muna zazzagayawa jihohi dabam-dabam domin taimaka wa mutane marasa galihu. Kwanannan muka dawo daga wasu garuruwa a jihar Kaduna sannan kuma za mu tafi wasu a jihar Neja domin ci gaba da wannan aiki da muke yi.

Share.

game da Author