Abubuwan da iyaye za su yi don gujewa haihuwar da baya iya tafiya, da kuma kumburarren kai

0

Shugaban kungiyar da ke yaki da fadakar da mutane kan cutar‘SpinaBifida and Hydrocephalus Care Foundation (SHCF)’ Olubunmi Lawal ta ce duk shekara akan haifo jarirai dauke da cutar‘Spina Bifida da ‘Hydrocephalus’ da suka kai miliyan 3.2 a duniya sannan 276,000 daga cikin su na mutuwa.

A jawabin ta a Abuja Olubunmi Lawal ta bayyana cewa cutar ‘Spina Bifida’ cuta ce dake hana kashin bayan jariri girma yadda ya kamata tun yana ciki saboda rashin samun wasu sinadarori dake taimakawa wajen haka sannan cutar ‘Hydrocephalus’ cuta ce dake tara ruwa a cikin kan jaririn wanda ke sanya kan kumburi.

Ta ce jariran da aka Haifa da irin wannan matsaloli na bukatan kula har na tsawon rayuwar su domin su rayu.

Olubunmi Lawal ta ce a yanzu hakan ba a gano maganin da zai sa a samu waraka daga cutar ba amma mata masu ciki za su iya shan maganin da ake kira ‘Folic Acid’ domin hana aukuwar cututtukan.

Share.

game da Author