Sakamakon bijire wa umarnin kotu, an tsare dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a Ɗakin ajiye firsinoni a Legas.
An tsare Aminu ne a yau Laraba, bayan yanke hukuncin ayi haka da kotun Majistare da ke unguwar Tinubu, a Legas.
An tuhumi Aminu da bijire wa umarnin da mai shari’a Kikelomo Ayeye ta ba shi a ranar 11 Ga Oktoba, 2017, da ya gabatar da dan sa da ya dauke daga tsohuwar matar sa Fatimo Bolori.
A ranar 11 Ga Oktoba ce alkali Ayeye ya umarce shi da ya gabatar da yaron mai suna Amir mai shekaru shida, yau Laraba a kotu domin a fara sauraren karar da ke tsakanin sa da matar sa Fatimo da suka rabu tun 2011.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ruwaito cewa da aka koma kotu yau, an shaida wa alkalin cewa bangarorin biyu sun amince su sasanta junan su a waje.
Sai dai kuma nan da nan sai lauyan Fatimo ya mike ya ce wa alkali shi dai wadda ya ke karewa ba ta sanar da shi cewa ta janye kara ko amincewar ta a sasanta a waje ba.
Jin haka, sai alkali ta juya wajen Aminu, ta ce masa tunda ya ki zuwa da yaro a kotu, to ya bijire wa doka. Nan take ta ce a tsare shi a dakin ajiyar masu laifi a kotu.
Alkali ta kuma tsaida shari’ar har sai an gabatar da yaron a kotu.
Tun da Aminu Atiku Abubakar ya rabu da Fatimo cikin 2011, ‘ya’yan su su na hannun ta, a bisa yarjejeniyar cewa a rika barin su na zuwa hutu a wurin mahaifin su.
Bincike ya tabbatar da cewa cikin 2013 mahaifin na su ya dauke su da nufin tafiya hutu da su kasar waje, amma daga lokacin bai sake maida su wurin mahaifiyar su ba.