Korar Babachir ya wanke mu sal – Inji APC

0

Darektan yada labaran jam’iyyar APC Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar APC ta wanke kanta ko ba sabulu game da koran tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal daga aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Ya fadi haka ne ranar Litini a Abuja da yake hira da manema labarai inda ya kara da cewa hakan da shugaban kasa Buhari ya yi ya yi daidai.

” A kwanakin baya mutane sun yabi koran da shugaban kasa ya yi wa Abdulrasheed Maina amma duk da hakan sai da suka yi ta korafi kan dalilin yin shiru da akayi game da harkallar Babbachir Lawal.”

” Hakan da shugaban kasa ya yi ya nuna cewa shugaban kasa ba zai nuna wariya ba kan yaki da yake yi da cin hanci da rashawa da gwamnatin sa keyi.”

Shugaban kwamitin dake shawartan shugaban kasa akan harkokin cin hanci Itse Sagay ya ce tun tuni ya kamata a kori Babachir daga aiki.

Share.

game da Author