Majalisar Dattawa ta koka kan halin da asibitocin kasar nan ke ciki

0

Majalisan dattijai ta koka kan halin da asibitoci mallakin gwamnatin tarayya ke ciki inda ta yi kira ga ma’aikatar kudi da ta ware isassun kudi domin fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Sanata Monsurat Sumonu dake wakiltan Oyo daga jam’iyyar APC ta jagoranci muhawaran a zauren majalisar.

Monsurat ta ce duk da matsayin da Najeriya ta kai a Afrika abun kunya ne a ce fannin kiwon lafiya na fama da matsalolin rashin isassun asibitoci da sauran su.

Ta kuma kara da cewa kasafin kudin shekara 2017 ta ware naira miliyan 308, 464, 276.782 domin fannin kiwon lafiya amma duk da hakan asibitocin gwamnatin kasa na fama da karancin magunguna da rashin kayan aiki.

“Ina amfanin gina ko kuma gyara asibitocin dake mallakin gwamanti idan basu da kayan da za su ceto rayukan mutane.?”

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa Ali Wakili daga jihar Bauchi yace babu yadda kasan za ta iya kawar da talauci idan bata da ingantaciyyar fannin kiwon lafiyan ta ba.

Ya kuma yi kira ga sauran sanatocin da su taimaka wajen ganin an kafa dokar ware kashi 1 bisa 100 cikin kudin da kasan ke samu domin fannin kiwon lafiya.

Share.

game da Author