Gwamnatin jihar Kebbi ta ware naira miliyan 900 don gyara gidajen yada talabijin da rediyo mallakar jihar.
Abubakar Dakingari, ya sanar da hakan ne ranar Laraba inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince ta gyara gidajen yada labaran ne ganin cewa mutanen jihar ba sa samun labarai yadda ya kamata.
Dakingari ya ce sarkin Yauri Zayyanu Abdullahi na cikin mutanen da suka kai kukan su fadar gwamnatin jihar inda ya bayyana cewa mutanen masarautarsa basa samun labarai yadda ya kamata.
” Sauraron rediyo ko kuma talabijin na taimakawa mutanen karkara wajen sanin abin dake faruwa cikin kasan da waje.”