Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa yankin Arewa fa ba ta wani tsoro ko fargabar sake fasalin kasar nan. Tambuwal ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN haka ne yau Laraba, a Kaduna.
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce Arewa ba ta tsoron a sake fasalin Najeriya, kamar yadda ake ta Kira da a yi zama domin sauya wa kasar fasali.
Ya yi wannan kalami ne da ya ka jawabi a wurin wani taron kwanaki biyu wanda Cibiyar Binciken da Ci Gaban Arewa ta shirya a garin Kaduna.
Tambuwal ya ce Arewa ba ta fargabar duk ma abin zai iya wakana ko yadda yankin Arewa zai kasance bayan an sake fasalin.
“Masu gani ko tunanin cewa wai Arewa na tsoron a sauya fasalin kasar nan, ko don ta na cin moriya da amfana daga tsarin faderaliyya da ake kai a yanzu, wannan ba gaskiya ba ne.”
“Bari ma na kara fitowa na jaddada maku cewa Arewa ta na maraba lale da sake fasalin kasar nan kamar yadda kowa da kuma kowane yanki ke yi”
“Sai dai kuma mu ba za mu rika yin babatu, kamar yadda wasu ke yi ba.
“Mu dai mun hakkake da cewa duk wani mataki kon matsaya da za mu dauka ko wacce za mu cimma, to lallai za ta kasance a kan tsari da ka’ida ta ke, ta yadda sakamakon da za a fitar zai zama alheri a gare mu.”
Ya kara da cewa za a bi jihohin Arewacin kasar nan 19 daya bayan daya ana bayyana sakamakon abin da kwamitin su ya tattauna dangane da batun sake fasalin kasar nan wanda shi ya ke jagoranta.
“Ni a nawa tunanin a matsayin mu na ‘yan kasa daya al’umma daya, ya kamata tashin farko tukunna ma mu fara bayyana mene ne sake fasalin dungurugum domin mu san ma’anar sa.
“Mu na fatan kasancewa a kasa mai yalwa, zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda adalci zai rika tabbata, yadda kowa zai iya zama da neman abincin sa a duk inda ya ke son zama.”
“Na yi imani da cewa kowace jiha a fadin kasar nan na da fannin da ta zarce saura, ita kuwa dama rayuwa cuda-ni-in-cude-ka ce. Ta inda wani ya fi ka, kai ma za ka ga ka fi shi a wani bangaren.”
Daga nan sai Tambuwal ya yi roko ga masu shirya taron da su gabatar da shawarwari masu ma’ana wadanda za su kara inganta dankon zumuncin dorewar hadin kan kasar nan.
Taken wannan taro shi ne: “Makomar Arewa a Dunkulliyar Najeriya.” An shirya taron ne da hadin guiwa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello.
Sauran kungiyoyin da su ka halarci taron sun hada da Kungiyar Dattawan Arewa, Kungiyar Wakilan Arewa, Kungiyar Tuntuba ta Arewa, CODE Group, Ku Tashi Mu Farka ‘Yan Arewa, Jam’iyyar Matan Arewa da kuma Kungiyar Matasan Arewa.
Discussion about this post