Kashi 86 bisa 100 na ‘yan gudun hijira na fargaban komawa garuruwan su

0

Kungiyoyi bada agaji na ‘Norwegian Refugee Council’ NRC, ‘REACH Initiative’da na ‘protection sector’ sun hada guiwa kan gudanar da bincike domin gano ra’ayoyin ‘yan gudun hijira game da komawa gidajensu.

A binciken da suka gudanar mai taken “Too Scared to Return” ya nuna cewa kashi 86 bisa 100 na ‘yan gudun hijiran dake zama a sansanonin jihar Barno na fargaban komawa garuruwansu.

‘Yan gudun hijiran sun ce suna fargaban komawa garuruwan su ne saboda tsoron sauran burbudin aiyukkan Boko Haram da ake fama da shi.

Shugaban kungiyar NRC Jan Egeland ya ce bai kamata a yi kunen uwar shegu da ra’ayoyin da suka samu daga wajen ‘yan gudun hijiran ba sakamkon binciken da suka yibinciken ba.

Ya ce duk da matsalolin da ake fama da su a cikin sansanonin bai kamata a tilasta wa ‘yan gudun hijaran sai sun koma garuruwansu ba tukuna.

“Kamata a yi a yi hakuri a ci gaba da kula da su har sai sun gamsu su koma garuruwan su da kansu.”

Jan Egeland ya ce binciken ya kara nuna cewa wasu cikin ‘yan gudun hijiran sun ce koda gwamnati ta kawar da Boko Haram gaba daya a jihar za su ci gaba da zama a Maiduguri.

” Mafi yawan mu Boko Haram sun kona mana gidajen mu a kauyukan mu wanda hakan ya sa baza mu koma ba.”

Share.

game da Author