Sojoji sun kwato shanu da tumakai 510 daga hannun barayi

0

Zaratan sojojin runduna ta 1 da ke Kaduna, sun kwato shanu da tumakai 510 daga hannun barayin shanu bayan sun yi artabu da suka yi.

Kakakin Sojoji Sani Usman ne ya bayyana haka a yau Laraba. Ya ce sojoji sun samu nasarar ceto shanu 269 da kuma tumakai 241, wadanda ya ce ana nan ana shirin damka su ga wadanda ke da su.

Idan ba a manta ba, sojoji sun samu nasarar karbo wasu dabbobi har 157 bayan sun kafsa da barayin shanu a Dajin Kabiru, da ke cikin Karamar Hukumar Bakura a jihar Zamfara.

Burgediya Usman ya kuma kara da cewa dakarun da ke “Operation Saran Daji” sun yi artabu da wasu barayin shanun a Kauran Mota da ke cikin karamar hukumar Anka, bayan an labarta musu mabuyar barayin, inda nan da nan su ka bi sawu.

Ya ce barayin da kan su, su ka gudu bayan sun ga cewa ba za su iya fada da sojojin ba.

A wani labarin kuma, Usman ya ce dakarun sojoji sun hadu da jami’an SSS inda suka kwato makamai a dajin cikin karamar hukumar Dandume cikin jihar Katsina.

Share.

game da Author