‘Yan sanda sun cafke motoci biyu makare da makamai a Zamfara

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta bayyana cewa ta kama wasu motoci biyu makare da makamai a cikin sassan jihar.

Kakakin yada labarai na rundunar, Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a Gasau, babban birnin jihar.

Ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai, NAN cewa daga cikin abubuwan da aka samu a tattare da su, akwai bindigogi kirar AK47 guda uku, kakin sojoji dinkakku, bindiga kirar fistol, kananan bindigogi kirar cikin gida, manyan jigidar albarusai da kuma tulin albarusai masu yawa.

Ya ce akwai kuma kudi naira 103, 435, katin cirar kudi na ATM, katinan jefa kuri’a, da kuma tambarin sitamfi na Kungiyar Masu Kiwon Shanu na Jihar Filato, shiyyar Karamar Hukumar Bukuru.

Shehu ya kara da cewa ‘yan sanda masu sintiri ne su ka kama direban motar daya, wani dan asalin kauyen Birnin-Yero cikin Karamar hukumar Shinkafi a jihar Sokoto.

Daya wanda aka kama kuwa dan asalin karamar hukumar Bassa ne ta jihar Filato. An same shi da bindigogi biyu, jigidan albarusai biyar da kuma albarushi har jigida 165.

An kama shi da kudi naira 68,750,katin ATM, rajistar zabe uku, kakin sojoji da kuma wayoyin hannu masu yawa. Shi wannan a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, an kama shi ne a kan hanyar Kaura-Namoda zuwa Jibiya.

A wata sabuwa kuma, gwamnan jihar Abdul’aziz Yari ya nuna fushin sa ga jami’an tsaron jihar danagane da yadda harkar tsaro ta lalace a Zamfara.

Ya nuna wannan fushin ne a lokacin da yake wani taro da shugabannin hukummin tsaron jihar.

Gwamnan yace akwai matukar damuwa da tashin hankali ganin yadda matsalar tsaro ke kara yawaita a Zamfara.

Share.

game da Author