Mutane 7 sun mutu a Shinkafi daga shan faten tsaki

0

Wasu mazauna garin Shinkafi karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara sun rasa rayukansu bayan sun sha faten tsaki.

Mukaddashin gwamnatin jihar Abdullahi Shinkafi ya sanar da haka wa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Gusau.

Ya ce wai wata mata ce ta girka faten tsaki inda ganyen albasar da ta hada faten dashi ya kamu da wata guba ba ta sani ba.

Ya ce matan, ‘ya’yanta shida da wani makwabcinsu sun mutu sannan wasu na kwance a asibiti har yanzu.

Abdullahi Shinkafi ya ce gwamnatin jihar ta aika da wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya domin gudanar da bincike akan dalilin mutuwan mutanen.

Da yake yi wa iyalan wadanda suka rasu, Abdullahi Shinkafi ya yi kira ga mutane da su kula da abincin da suke ci sannan su tabbata muhallinsu na tsaftace a kowani lokaci.

Share.

game da Author