Shugaban hukumar kula da asibitocin jihar Bauchi Abdulaziz Manga ya ce jihar Bauchi na fama da karanci likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya.
Manga ya ce cikin ma’aikata 6000 da suke da shi suna da likitoci 67 ne sannan a haka suna da ma’aikatan jinya 875 da kwararrun masu ilimin sarafa magani 15.
Ya ce hakan yayi wa jihar kadan matuka musamman ganin cewa dole mutanen da ke da bukatar hakan na da yawan gaske.
Manga ya ce kusan yanzu ma’aikaciyar jinya da ne ke kula da kusan asibiti kaf in da ake bukatar akalla 4 domin haka.
” Manyan asibitoci 27 muke da su da wasu kananan cibiyoyin kiwon lafiya masu yawa a jihar Bauchi. Muna bukatar akalla ma’aikaciyar kiwon lafiya 4 ne da masu bada magani a kowani asibiti.”
Daga karshe ya roki ma’aikatan da su mai da hankali a wajen ayyukansu.
Discussion about this post